Connect with us

News

Za a gudanar da addu’o’in cika shekara da rasuwar Buhari a ranar Litinin

Published

on

Tsohon mai taimaka wa tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari

Tsohon mai taimaka wa tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kan harkokin yaɗa labarai, Bashir Ahmad, ya sanar da shirin gudanar da addu’o’i da taron tunawa da cika shekara ɗaya da rasuwar tsohon shugaban ƙasar.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Bashir Ahmad ya ce za a gudanar da taron ne a ranar Litinin, 13 ga Yulin 2026, domin tunawa da rayuwa, gudunmawa da kuma hidimar da Buhari ya yi wa Najeriya.

Jami’an Ƴansanda Sun Kama Mahaifin Prince Adeyemi Adeniyi, Mutumin Da Ake Zargi Da Kafa Hukumar Bogi

Ya bayyana Buhari a matsayin shugaba mai jajircewa, gaskiya, ɗa’a da kishin ƙasa, yana mai cewa irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban Najeriya za ta ci gaba da kasancewa cikin tarihi.

 

A cewarsa, yan uwa, abokai, tsoffin hadimai, abokan siyasa da sauran yan Najeriya za su hallara domin yin addu’o’i tare da roƙon Allah Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya sa Aljannar Firdausi ta zama makomarsa, sannan Ya ba iyalansa da al’ummar Najeriya haƙurin rashinsa.

Advertisement

Marigayi Muhammadu Buhari ya rasu ne a ranar 13 ga Yulin 2025 yana da shekaru 82, bayan fama da jinya a wani asibiti da ke birnin London na ƙasar Birtaniya.

Daga bisani aka dawo da gawarsa Najeriya, inda aka yi masa jana’iza a garinsu na Daura a Jihar Katsina.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending