News
An Kama Wani Mutum Bisa Zargin Fataucin Jaririn Gwaggon biri A Kano
Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta kama wani mutum da ake zargi da safarar dabbobin daji ba bisa ka’ida ba, tare da ceto wani jaririn Gwaggon biri a wani samame da ta kai a unguwar Kofar Mata da ke Jihar Kano.
Hukumar ta bayyana cewa an gudanar da aikin ne a ranar 7 ga watan Yuli bayan shafe makonni ana tattara bayanan sirri da sanya ido kan ayyukan waɗanda ake zargi.
Gwamnatin Tarrayya Ta Sanar Da Ceto Ɗaliban Da Aka Sace A Oyo
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta a ranar Alhamis, hukumar ta ce jami’an Ofishin Musamman na Yaƙi da Fataucin Dabbobin Daji na Sashen Leken Asiri na Kwastam ne suka gudanar da samamen tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Focused Conservation, Rundunar ‘Yan Sandan Kwastam da kuma jami’an Kwastam na Yankin Kano/Jigawa.
Jami’in da ke jagorantar ofishin, Mataimakin Kwanturola na Kwastam, Anuhu Mani, ya ce an garzaya da jaririn gorilar da aka ceto zuwa cibiyar kula da dabbobi, inda ake ba shi kulawar likitoci ta musamman tare da shirin farfaɗo da lafiyarsa.
Ya ce samamen ya kuma yi nasarar daƙile ayyukan wata ƙungiyar da ake zargi da safarar dabbobin daji masu kariya a yankin Kano.
Ya ce bincike kan lamarin na ci gaba da gudana domin gano sauran mutanen da ake zargi da hannu a wannan haramtacciyar harka. Sai dai ya ce hukumar ba za ta bayyana sunan wanda aka kama ko wasu ƙarin bayanai kan samamen ba a yanzu, domin kada hakan ya kawo cikas ga binciken da ake yi.
-
Uncategorized6 days ago
Samar Da Zaman Lafiya, Ayyukan Ci Gaba Sun Isa Shugaba Tinubu Ya Samu Wa’adi Na Biyu — Kwankwaso
-
News5 days ago
Aƙalla Mutane 40 Sun Mutu Bayan Kifewar kwale-kwale A Sokoto
-
News21 hours ago
Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad
