News
A Kasa Mai Mabiya Addinai Daban-daban, Bai Kamata A Sanya Addini Cikin Rudanin Siyasar Da Ke Cike Da Takaddama Ba. —Sheikh Gumi
Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya yi kira da a raba addini da siyasar jam’iyyu a Najeriya, yana mai cewa bai kamata a mayar da addini wani ɓangare na rikicin siyasa ba.
Sheikh Gumi ya bayyana cewa, a ƙasa mai mabiya addinai daban-daban kamar Najeriya, ya kamata a yi taka-tsantsan wajen haɗa batutuwan addini da siyasar jam’iyyu, domin kauce wa rikici, ƙiyayya da rarrabuwar kawuna.
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
Malamin ya bayyana hakan ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan rawar da addini ke takawa a siyasar Najeriya, musamman a daidai lokacin da fafatawar siyasa ke ƙara zafi gabanin zaɓuka masu zuwa.
Ya ce ra’ayoyin addini da siyasar jam’iyyu ya kamata a tafiyar da su daban, domin kada a yi amfani da addini wajen cimma manufofin siyasa ko kuma tayar da hankulan al’umma.
Da yake mayar da martani kan matsayar da Sheikh Yahya Jingir ke nunawa kan wasu batutuwan siyasa, Gumi ya ce ya kamata a fahimci yanayin da Jingir yake ciki, musamman ganin yadda yake kallon matsalolin da suka shafi addininsa da al’ummarsa.
Ya jaddada cewa bambancin ra’ayi a siyasa ba ya kamata ya zama dalilin haifar da ƙiyayya tsakanin mabiya addinai ko ƙungiyoyin al’umma, yana mai kira ga shugabanni da malamai da su taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
A cewarsa, Najeriya tana buƙatar shugabanni da masu ruwa da tsaki waɗanda za su fifita zaman lafiya, adalci da haɗin kan al’umma sama da muradun siyasa ko na jam’iyya.
-
News7 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News7 days ago
Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomin Bagwai, Rogo Da Bebeji
