Connect with us

News

Tafiye-tafiyen Shugaba Tinubu Ya  Lakume Sama Da Naira Biliyan 37 —Bincike

Published

on

Tinubu 3 (1)

Fadar Shugaban Ƙasa ta kashe sama da Naira biliyan 37.64 kan tafiye-tafiye da sauran abubuwan da suka shafi zirga-zirgar Shugaba Bola Ahmed Tinubu cikin gida da wajen Najeriya cikin shekaru uku.

Wani bincike kan bayanan kashe-kashen gwamnati da cibiyar GovSpend, wadda ke bibiyar yadda ake kashe kuɗaɗen gwamnati, ta fitar ya nuna cewa an kashe jimillar N37,639,227,853.51 daga Yunin 2023 zuwa Afrilun 2026.

Gwamnan Plateau Ya Hana Ayyukan HISBA A Jos

Binciken ya haɗa da kuɗaɗen tafiye-tafiyen shugaban ƙasa, dabarun gudanar da balaguro, canjin kuɗaɗen waje da sauran abubuwan da suka shafi tafiye-tafiyen fadar shugaban ƙasa.

Bayanan sun nuna cewa an kashe N9.18bn a rabin shekarar 2023, yayin da aka kashe N25.27bn a shekarar 2024. A shekarar 2025 kuma an kashe N2.70bn, sannan aka kashe N477.45m tsakanin Janairu da Afrilun 2026.

Shekarar 2024 ce ta fi kowace shekara yawan kuɗin da aka kashe, inda babban ɓangaren kuɗin ya tafi ne wajen rabon kuɗaɗen waje da kuma tallafa wa Presidential Air Fleet, wato rundunar jiragen Shugaban Ƙasa.

Advertisement

Bayanan da aka bincika sun nuna cewa tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayun 2023, Tinubu ya yi tafiye-tafiye zuwa ƙasashe daban-daban domin halartar tarukan ƙasa da ƙasa, ganawar diflomasiyya, tattaunawar kasuwanci da sauran ayyukan gwamnati.

A cewar bayanan tafiye-tafiye, Tinubu ya yi tafiye-tafiye 51 zuwa ƙasashen waje, inda ya ziyarci akalla ƙasashe 30, kuma ya shafe kimanin kwanaki 261 a wajen Najeriya tun bayan hawansa mulki.

Sai dai sabon hutun makonni uku da ya fara zuwa Turai a ranar Lahadi ya ƙara yawan tafiye-tafiyen zuwa 52.

A halin da ake ciki, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki lokacin da Shugaba Tinubu ya zaɓa domin tafiyar, yana mai cewa ya kamata shugaban ya kasance a gida domin fuskantar matsalolin da ƙasar ke ciki.

Sai dai Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Sadarwa, Sunday Dare, ya kare tafiyar, yana mai cewa shugaban ya cancanci hutun domin samun damar sake ƙarfafa jiki gabanin fara wani zangon ayyuka da ya haɗa da shirye-shiryen zaɓen 2027.

Fadar Shugaban Ƙasar ta ce duk da hutun, Tinubu zai ci gaba da karɓar rahotanni daga ministoci da shugabannin hukumomin tsaro tare da sanya ido kan harkokin mulkin ƙasar.

Advertisement

 

 

DAILY TRUST 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending