News
Gwamnan Kano Ya Taya Abdulmumin Jibrin Kofa Murnar Cika Shekaru 50
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya taya ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Ƙananan Hukumomin Kiru/Bebeji a Majalisar Tarayya, Hon. Dr. Abdulmumin Jibrin Kofa, murnar cika shekaru 50 da haihuwa.
Wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Litinin ce ta bayyana hakan.
Gwamna Yusuf ya bayyana Kofa a matsayin ɗan asalin Kano nagari kuma fitaccen ɗan ƙasa, wanda gudummawar da yake bayarwa ga al’ummarsa, Jihar Kano da Najeriya ta cancanci yabo da girmamawa.
“Wasu Daga Cikin Mutanen Da Buhari Ya Amince Da Su Ne Suka Ci Amanarsa” — Lawal Daura
Gwamnan ya yaba da irin rawar da Kofa ke takawa a Majalisar Dokoki ta Ƙasa, inda ya taɓa riƙe muƙamai daban-daban, ciki har da Shugaban Kwamitocin Kuɗaɗe, Kasafin Kuɗi, Sufuri da Harkokin Ƙasashen Waje, yayin da a halin yanzu yake jagorantar Kwamitin Gidaje da Muhalli.
A cewar Gwamna Yusuf, Kofa ya nuna ƙwarewa wajen gudanar da ayyukan majalisa ta hanyar wakilci nagari, bayar da shawarwari da kuma ƙaddamar da shirye-shiryen da suka shafi inganta rayuwar al’ummar da yake wakilta.
Ya kuma yaba da gudummawar da Kofa ya bayar a ɓangaren gidaje da cigaban ƙasa a lokacin da yake aiki a Hukumar Kula da Gidaje ta Tarayya.
Gwamna Yusuf ya kuma yaba da yadda ɗan majalisar ke cigaba da mayar da hankali kan cigaban al’umma, musamman ta hanyar shirye-shiryen tallafa wa matasa, mata, manoma, ’yan kasuwa da sauran masu ƙaramin ƙarfi.
Ya ce shirye-shiryen tallafin da Kofa ke gudanarwa, waɗanda suka haɗa da samar da kayan aikin dogaro da kai, tallafin kasuwanci, koyar da sana’o’i, tallafin ilimi da shirye-shiryen noma, sun taimaka wajen samar da damammaki ga dimbin al’ummar mazabarsa domin inganta rayuwarsu.
Gwamna Yusuf ya ce: “Kai ɗan majalisa ne nagari wanda ka nuna ƙwarewa wajen wakiltar al’ummarka. Shirye-shiryen tallafa wa jama’a da bunkasa rayuwar al’ummar Ƙananan Hukumomin Kiru/Bebeji da kake yi abin a yaba ne kuma ya cancanci a yi koyi da shi.”
Gwamnan ya ƙara bayyana Kofa a matsayin ma’aikacin gwamnati wanda ya haɗa nauyin ayyukan majalisa da kai-tsaye wajen hulɗa da al’umma, domin tabbatar da cewa an saurari buƙatu da matsalolin waɗanda yake wakilta.
Ya ce ƙwarewar Kofa a matsayin ɗan kasuwa, malami, ma’aikacin gwamnati da ɗan majalisa ta ba shi damar bayar da muhimmiyar gudummawa wajen tattauna batutuwan ƙasa da kuma matsalolin da suka shafi Jihar Kano.
Gwamna Yusuf ya ce: “Bayan ka cimma abubuwa da dama a lokacin da ka kai shekaru 50, Jihar Kano tana alfahari da kai, tare da yaba da irin gudummawar da kake bayarwa wajen ci gaban jiharmu da ƙasarmu baki ɗaya.”
Gwamnan ya yi wa Dr. Abdulmumin Jibrin Kofa fatan ƙarin shekaru masu yawa cikin ƙoshin lafiya, farin ciki da nasara. Ya kuma roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya ƙara ba shi hikima da ƙarfi domin ci gaba da yi wa al’umma hidima.
Haka kuma, Gwamna Yusuf ya yi addu’ar Allah Ya buɗe wa Kofa ƙarin damammaki da za su ba shi damar ci gaba da bayar da gudummawa wajen haɓaka da bunƙasa Jihar Kano da Najeriya.
