Connect with us

News

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mutane Biyu Kan Zargin Hallaka Ibrahim Khalil Danshagamu A Kano 

Published

on

IMG 20260909 234510 516

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan Ibrahim Khalil Danshagamu, wanda aka kashe a Unguwar Gaida da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso ta jihar.

Mai magana da yawun rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, inda ya ce an kama waɗanda ake zargin ne yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.

Kai Hari Kan ’Yan Jarida , Hari Ne Kan Dimokuraɗiyya — Abbas Ibrahim

Rahotanni sun ce wasu mutane sun haura gidan marigayin Ibrahim Khalil Danshagamu a Unguwar Gaida, inda ake zargin sun kai masa hari tare da yi masa yankan rago.

Kiyawa ya ce rundunar ta samu haɗin kai daga jami’an Vigilante na Gaida, waɗanda suka taimaka wajen samar da muhimman bayanai da za su taimaka wajen gudanar da binciken.

Ya ƙara da cewa rundunar na ci gaba da faɗaɗa bincike domin gano cikakkun bayanai kan yadda lamarin ya faru da kuma gano sauran waɗanda ka iya kasancewa da hannu a kisan.

Advertisement

Mai magana da yawun rundunar ya ce binciken na gudana ne bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, tare da tabbatar da cewa za a ɗauki matakin da ya dace bayan kammala bincike.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending