Connect with us

News

Gidauniyar Festula Ta Tallafa Wa Mata 50 Da Suka Warke Daga Yoyon Fitsari

Published

on

IMG 20250203 130633 995 768x346

Gidauniyar Festula Foundation ta tallafa wa mata 50 da suka warke daga lalurar yoyon fitsari a Jihar Kano, da kayan sana’o’i domin taimaka musu wajen dogaro da kansu.

Tallafin da aka rabawa matan ya haɗa da kekunan ɗinki, injinan markade, kaji, kayan kitso, man gyada da sauran kayayyakin sana’o’i.

Mun Sha Fitsarinmu Don Mu Tsira Da Ranmu — Wanda Ya Tsira Daga Mutuwar Mutane 37 A Neja

Wakiliyar Kwamishiniyar Harkokin Mata ta Jihar Kano, Dr Halima B.B. Faruk, ta bayyana cewa gwamnatin jihar na farin ciki da yadda matan suka samu magani kuma suka warke daga lalurar.

Ta ce baya ga yi wa matan magani, an kuma koyar da su sana’o’i tare da ba su kayan aiki, domin su samu hanyar samun abin dogaro da kansu.

Dr Halima ta kuma yi kira ga al’umma da su daina kyamar matan da suka kamu da yoyon fitsari, tana mai cewa wariya da kyama na iya kara jefa masu fama da matsalar cikin damuwa da ware kansu daga al’umma.

Advertisement

Ta ce gwamnatin Kano za ta ci gaba da tallafa wa mata masu fama da lalurar, tare da samar da kulawar da ta dace.

Shugaban Festula Foundation, Baba Musa Isah, ya ce gidauniyar tana gudanar da ayyukan taimaka wa mata masu fama da yoyon fitsari a sassan Najeriya, ciki har da yi musu tiyata kyauta.

Ya ce bayan samun waraka, gidauniyar tana koyar da matan sana’o’i tare da ba su kayan aiki domin su samu damar dogaro da kansu da sake komawa cikin al’umma.

Baba Musa ya ce duk da ƙoƙarin da ake yi na magance matsalar yoyon fitsari, har yanzu ana samun sabbin masu fama da lalurar, lamarin da ya sa gidauniyar ke ci gaba da gudanar da ayyukan wayar da kai da tallafawa marasa lafiya a sassan ƙasar.

Wasu daga cikin matan da suka samu waraka sun bayyana farin cikinsu, tare da godiya ga gidauniyar da gwamnatin Jihar Kano bisa tallafin da suka samu.

Sun ce samun magani da kuma koyon sana’a ya taimaka musu wajen sake komawa cikin al’umma da fatan samun abin dogaro da kansu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending