Connect with us

News

Mutum 332 Sun Kamu Da Cutar Mashaƙo A Gombe

Published

on

Gwamnatin Jihar Gombe ta fara gudanar da allurar rigakafin cutar mashaƙo bayan da mutane 332 suka kamu da cutar a ƙananan hukumomi huɗu na jihar

Ƙananan hukumomin da aka samu rahoton ɓarkewar cutar sun haɗa da Akko, Gombe, Kwami da Funakaye.

KANO:Wata Mata Ta Hallaka Mijinta Saboda Zai Mata Kishiya A Rogo

Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Gombe ta umarci shugabannin makarantu da su haɗa kai da jami’an lafiya wajen gudanar da aikin rigakafin, tare da wayar da kan ɗalibai da iyayensu kan hanyoyin kariya daga cutar.

A cewar bayanan, za a fara zagayen farko na rigakafin daga ranar 20 zuwa 24 ga Satumba 2026, yayin da za a gudanar da sauran alluran bisa tsarin da ma’aikatan lafiya suka tsara.

Cutar mashaƙo cuta ce mai saurin yaɗuwa wadda ke shafar hanyoyin numfashi. Ana iya yaɗa ta daga mutum zuwa mutum ta hanyar ɗigon yawu ko majina daga mai ɗauke da cutar, musamman yayin tari ko atishawa.

Advertisement

Hukumomin lafiya sun ƙara ƙaimi wajen gudanar da rigakafi da wayar da kan jama’a, musamman a makarantu, domin dakile yaɗuwar cutar da kare al’umma daga kamuwa da ita.

 

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending