Connect with us

News

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Budurwa Kan Zargin Garkuwa Da Kanta

Published

on

unnamed 52 1789896085 768x576

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Anambra ta kama wata budurwa mai shekaru 22, Nwachukwu Chidubem Blessing, bisa zargin shirya garkuwa da kanta domin karɓar kuɗin fansa daga iyalanta.

Ana zargin cewa lamarin ya sa iyalan budurwar suka biya kuɗin fansa har Naira miliyan uku, kafin jami’an tsaro su gano cewa an shirya lamarin ne.

Ya Kamata ’Yan Jarida Su Guji Rahotannin Da Ka Iya Haifar Da Tashin Hankali — KOMC ‎

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Tochukwu Ikenga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 20 ga Satumba, 2026.

Ya ce jami’an Rundunar Rapid Response Squad (RRS) da ke Awkuzu ne suka cafke wacce ake zargin bayan samun sahihan bayanan sirri.

A cewar Ikenga, jami’an sun samu bayanan ne yayin da suke gudanar da bincike kan rahoton sace mutumin da aka kai wa rundunar.

Advertisement

Ya ƙara da cewa binciken da jami’an suka gudanar ya kai ga gano cewa ana zargin budurwar da hannu wajen shirya sace kanta, lamarin da ya jawo biyan kuɗin fansar Naira miliyan uku.

 

 

 

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending