News
DSS, Sojoji da ’Yan Sanda Sun Kama Mutane Biyar Bisa Zargin Sace ’Yan NYSC 20 A Imo
Jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), tare da haɗin gwiwar sojoji da ’yan sanda, sun kama wasu mutane biyar da ake zargi da hannu wajen sace ’yan bautar ƙasa (NYSC) guda 20 a Jihar Imo.
An kama waɗanda ake zargin ne yayin samamen da jami’an tsaro suka gudanar bisa sahihan bayanan sirri a wasu wurare na jihohin Rivers da Abia, tsakanin ranar 10 zuwa 14 ga Oktoba, 2026.
Ƙofar Jirgin Sama Ta Ɓalle A Sararin Samaniya A Abuja
Rahotanni sun nuna cewa samamen ya gudana ne a birnin Port Harcourt na Jihar Rivers da kuma Ƙaramar Hukumar Aba ta Kudu a Jihar Abia.
Sai dai, wasu mutane uku da ake zargin suna da alaƙa da ƙungiyar sun tsere yayin samamen, duk da cewa sun samu raunukan harbin bindiga.
An sace ’yan NYSC 20 ɗin ne a ranar 1 ga Oktoba, 2026, lokacin da wasu ’yan bindiga suka tare motocin da suke ciki a kan hanyar Owerri zuwa Onitsha, a Jihar Imo.
A lokacin da lamarin ya faru, matasan na kan hanyarsu ta zuwa sansanonin horas da ’yan bautar ƙasa a jihohin Abia da Akwa Ibom.
Sai dai, jami’an tsaro sun samu nasarar kuɓutar da dukkan matasan a ranar 7 ga Oktoba, 2026, yayin wani samame da suka gudanar a ƙauyen Amakohia-Ubi da ke Jihar Imo.
Kamen na baya-bayan nan na zuwa ne yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da ƙoƙarin gano sauran waɗanda ake zargi da hannu a lamarin, tare da tarwatsa ƙungiyar da ake zargin ta aikata laifin.
Wata majiya daga jami’an tsaro ta bayyana kamen a matsayin wani gagarumin ci gaba a ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da laifukan sace mutane.
Majiyar ta kuma bayyana cewa ana sa ran za a gurfanar da waɗanda aka kama a gaban kotu domin fuskantar shari’a.
-
News4 days ago
Kwararren Mai Daukar Hoton Labari Maikatanga Ya Shiga Sahun Kwamitin Alkalan Gasar Wole Soyinka Ta 2026
-
News1 day ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News3 days ago
AWOHI Ta Raba Kayan Tallafi A Gidan Kula Da Tsofaffi Na Shahuci Dake Kano
