News
Hanyar Kaduna-Abuja Yanzu Haka Bata Da Hatsari, -CP Ya Tabbatarwa Da Masu Ababen Hawa
Daga maryam bashir musa
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna, CP, Yekini Ayoku, ya tabbatar wa da duk masu amfani da babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja cewa a yanzu ba ta da hadari.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige, a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, ya ce CP din ya ba da wannan tabbacin ne a lokacin da ya fara wani rangadin karfafa gwiwa da tantancewa na babbar hanyar.
Jalige ya ce kwamishinan ‘yan sandan ya samu rakiyar manyan jami’an ‘yan sanda na rundunar.
Ya ce, a yayin ziyarar, Ayoku ya tattauna da jami’an tsaro a wurare daban-daban a kan babbar hanyar da ta kasance mai cike da cunkoso.
Kazalika Jalige ya rawaito kwamishinan ‘yan sandan ya yabawa ‘yan sandan bisa ayyukan da suke yi wa kasa, yana mai ba su tabbacin cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya zata rika duba lafiyarsu a koda yaushe.
Mista Ayoku, ya shawarci jama’a da masu zirga-zirgar ababen hawa a kan babbar hanyar da a ko da yaushe su hanzarta kai rahoton abubuwan da ba a saba gani ba ko wadanda ake zargi don daukar matakin gaggawa.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
