Connect with us

News

Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90

Published

on

IMG 20261017 WA0004

Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyin Salula da Kayan Haɗinsu ta Ƙasa (AMPATN), reshen Jihar Kano, ta buƙaci Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) da ta dakatar da shirin karɓar kuɗaɗe kan wayoyin salula da toshe wasu wayoyi na tsawon kwanaki 90, domin ba wa masu ruwa da tsaki damar tattaunawa kan tsarin.

Ƙungiyar ta bayyana cewa ba ta adawa da rajistar wayoyin salula ko matakan da za su taimaka wajen kawar da wayoyin jabu da hana amfani da wayoyin sata, sai dai tana nuna damuwa kan kuɗaɗen da ake shirin karɓa da kuma tasirinsu ga ’yan kasuwa da masu sayen wayoyi.

ME YA SA GWAMNA ABBA YA CANCANCI WANI WA’ADIN MULKI

Sani Tasi’u Ibrahim, Shugaban Kwamitin Amintattu na Ƙasa na Ƙungiyar AMPATN ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Sakatariyar NUJ da ke Kano.

A cewarsa, bayanan da ƙungiyar ta samu sun nuna cewa ana shirin karɓar kusan Naira 670 kan kowace waya mai maɓallai, yayin da ake sa ran karɓar kusan Naira 4,000 kan kowace waya mai allon taɓawa.

Ya ce aiwatar da shirin ba tare da cikakkiyar tattaunawa da ’yan kasuwa ba, na iya jawo tashin farashin wayoyi tare da ƙara wa masu ƙananan sana’o’i nauyin tattalin arziki.

Advertisement

“Ba mu da wata matsala da yi wa wayoyi rajista. Muna goyon bayan kawar da wayoyin jabu daga ƙasar nan. Amma muna buƙatar a nuna mana dokar da ta ba da izinin karɓar waɗannan kuɗaɗe,” in ji shi.

Shugaban ya ƙara da cewa harkar kasuwancin wayoyin salula na samar da ayyukan yi ga matasa da dama, ciki har da masu gyaran waya, direbobi, masu jigilar kaya da masu gudanar da ƙananan shaguna.

Ya yi gargaɗin cewa aiwatar da shirin ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki ba, na iya tilasta wa wasu ’yan kasuwa rufe shaguna tare da jawo asarar ayyukan yi, lamarin da zai ƙara tsananta matsin tattalin arzikin da jama’a ke fuskanta.

Saboda haka, ya buƙaci NCC da ta fito fili ta bayyana tushen dokar da aka yi amfani da ita wajen tsara shirin, tare da wallafa ƙa’idojin aiwatar da shi da kuma jadawalin kuɗaɗen da aka amince da su.

 

Buƙatu biyar ga gwamnati

Advertisement

AMPATN ta gabatar da buƙatu guda biyar da ta ce za su taimaka wajen tabbatar da adalci da kare muradun ’yan kasuwa da masu amfani da wayoyin salula.

Buƙatun sun haɗa da dakatar da karɓar kuɗaɗen da ake shirin karɓa da kuma toshe wayoyi na tsawon kwanaki 90, domin ba da damar gudanar da tattaunawa tsakanin gwamnati, NCC da wakilan ’yan kasuwa.

Haka kuma, ƙungiyar ta buƙaci NCC da ta bayyana tushen dokar da ta ba da izinin karɓar kuɗaɗen, tare da tabbatar da cewa an tuntubi ’yan kasuwa kafin aiwatar da tsarin.

Sauran buƙatun sun haɗa da samar da hanyar ɗaukaka ƙara ga mutanen da aka toshe wa wayoyinsu bisa kuskure, da kuma tabbatar da cewa ana bin ƙa’idojin doka kafin ɗaukar matakan da za su shafi masu amfani da wayoyin.

Shugaban ya bayyana cewa ƙungiyar ta riga ta aika da wasiƙa ga NCC, tare da gabatar da ƙorafinta ga Majalisar Dattawa, Majalisar Wakilai da Gwamnan Jihar Kano.

Ya jaddada cewa ƙungiyar ba ta neman rikici da gwamnati, sai dai tana son a saurari ƙorafinta domin samar da mafita da za ta amfani dukkan ɓangarorin da abin ya shafa.

Advertisement

Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya, Majalisar Dokoki ta Ƙasa da Gwamnatin Jihar Kano da su shiga tsakani, domin tabbatar da cewa ƙoƙarin yaƙi da wayoyin jabu da na sata bai zama sanadin durƙushewar sana’ar sayar da wayoyi ko ƙara wa jama’a nauyin kuɗaɗen sayen waya ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending