Connect with us

News

Gwamnatin Kebbi Ta Yi Wa Malami Martani Kan Rahoton Talauci na UNDP

Published

on

IMG 20261019 WA0003

Daga Khadijat Saidu, Birnin Kebbi

Gwamnatin Jihar Kebbi ta caccaki tsohon Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami, SAN, kan amfani da rahoton talauci na Hukumar Ci Gaban Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP) wajen sukar gwamnatin jihar, tana mai cewa rahoton ya shafi lokacin mulkin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Alhaji Yakubu Ahmed Birnin Kebbi, wanda aka fi sani da Ahmed-BK, ne ya bayyana hakan ranar Asabar yayin ganawa da manema labarai a Birnin Kebbi.

Cin Hanci Ya Mayar da Kotunan Najeriya Kasuwannin Sayar da Hukunci — Tsohuwar Alƙaliyar Kotun Ƙoli

Ya zargi Malami da jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) da siyasantar da rahoton gabanin zaɓen 2027, yana mai cewa matsalolin talaucin da rahoton ya nuna sun samo asali ne tun lokacin gwamnatin Buhari.

Ahmed-BK ya kuma zargi tsohon ministan da hannu a gazawar tattalin arziki da kuma siyasantar da matsalar tsaro a jihar. Sai dai waɗannan zarge-zarge ne na kwamishinan, kuma ba su tabbatar da laifin Malami ba.

Advertisement

Da yake kare gwamnatin Gwamna Nasir Idris, kwamishinan ya ce gwamnatin ta zuba jari wajen tsaro, ta samar da motocin Hilux da babura ga jami’an tsaro, tare da ƙarfafa sansanonin sojoji a jihar.

Ya kuma lissafa ayyukan raya ƙasa da suka haɗa da gina hanyoyi, inganta lafiya da ilimi, tallafa wa manoma, ɗaukar malamai aiki da biyan tallafin karatu.

Ahmed-BK ya ce gwamnatin na ƙoƙarin rage talauci da gyara matsalolin da al’umma ke fuskanta, yana mai kira ga jama’a da su mara mata baya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending