Connect with us

News

IITA Ta Horar Da Manoma Sama Da 1,800 Kan Sabbin Dabarun Noman Zamani A  Kano ‎

Published

on

IMG 20261019 WA0040

Cibiyar Binciken Aikin Noma ta Ƙasa da Ƙasa (IITA), tare da haɗin gwiwar Ofishin Kula da Ayyukan Muhalli da Ƙasa (EPO) na Najeriya, ta horar da manoma sama da 1,800 a Jihar Kano kan sabbin fasahohin noma domin ƙara yawan amfanin gona da inganta samar da abinci.

‎Shirin ya haɗa da manoma daga ƙananan hukumomi 16 na shiyyar Kano ta Kudu, inda aka koya musu dabarun noman zamani da za su taimaka wajen inganta ayyukan gonakinsu da rage ƙalubalen da suke fuskanta, musamman wajen noma a lokacin rani.

‎Rashin Nagarta Ce Ta Sa Buhari Ya Ki Goyon Bayan Takarar Shugaba Tinubu —Baba-Ahmed

‎An gudanar da horon da gwajin sabbin fasahohin noma a garin Hamdullahi da ke Ƙaramar Hukumar Albasu, inda aka nuna wa manoma yadda za su yi amfani da ingantattun nau’ikan iri da sauran dabarun noma domin samun amfanin gona mai yawa.

‎Da yake jawabi a wajen shirin, Jami’in Gudanar da Ayyuka na IITA, Farfesa Lucky Omoigui, ya ce an tsara horon ne domin ƙara wa manoma ilimi kan ingantattun nau’ikan iri da dabarun noman zamani.

‎Ya bayyana cewa sama da mutane 1,800 ne suka amfana da shirin, yana mai cewa ana sa ran ilimin da suka samu zai ƙarfafa noman rani da kuma inganta samar da abinci.

Advertisement

‎Omoigui ya buƙaci manoman da suka halarci horon da su yi amfani da ilimin da suka samu wajen inganta ayyukan gonakinsu da ƙara yawan amfanin gona.

‎A yayin shirin, an kai manoman gonakin gwaji domin nuna musu yadda ake amfani da sabbin dabarun noma wajen shuka amfanin gona da suka haɗa da wake, masara, waken soya, gyada, dawa da shinkafa.

‎A nasa jawabin, wakilin EPO, Bashir Ibrahim Umar, ya ce noma na taka muhimmiyar rawa wajen rage talauci da samar da ayyukan yi, musamman ga matasa a Najeriya.

‎Ya jaddada muhimmancin ci gaba da wayar da kan manoma tare da samar musu da ilimin da zai taimaka musu wajen rungumar sabbin fasahohin noma domin inganta rayuwarsu.

‎Shi kuwa Garba Ayuba, wanda ya wakilci Shugaban Ƙaramar Hukumar Albasu, Garba Aliyu Hungu, ya bayyana farin cikinsa kan gudanar da shirin a yankin, tare da buƙatar manoma su yi amfani da dabarun da aka koya musu.

‎Haka kuma, Daraktan Yankin Gaya na Hukumar Bunƙasa Aikin Noma ta Jihar Kano (KNARDA), Danjuma Uba, ya bayyana jin daɗinsa kan yadda manoma suka nuna sha’awar koyon sabbin dabarun noma.

Advertisement

‎Ya ce haɗin gwiwa tsakanin hukumomin da ke tallafa wa harkar noma da manoma na da muhimmanci wajen tabbatar da ɗorewar amfani da fasahohin zamani.

‎A nasa ɓangaren, Alhaji Saidu Abdulkadir Hamdullahi, wanda aka yi amfani da gonarsa wajen gwada sabbin nau’ikan iri, ya ce a baya wasu mutane ba su yi imanin cewa za a iya gudanar da noma mai inganci a lokacin rani ba.

‎Sai dai ya bayyana mamaki da farin cikinsa kan yadda aka samu damar shuka amfanin gona a gonarsa a lokacin rani, yana mai cewa hakan ya ƙara masa ƙwarin gwiwa.

‎Ya gode wa IITA da abokan haɗin gwiwarta bisa horon da aka bai wa manoma, yana mai cewa sun ƙara samun ilimi kan shuka iri, amfani da taki da sauran dabarun noman zamani.

‎A cewarsa, sabon ilimin zai taimaka musu wajen inganta amfanin gonakinsu da ƙara kuɗin shiga.

Shirin na daga cikin ƙoƙarin bunƙasa harkar noma ta hanyar ƙarfafa manoma su rungumi sabbin fasahohi domin inganta samar da abinci da rage talauci a Najeriya, musamman a yankunan da ke fuskantar ƙalubalen ƙarancin ruwa.

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending