Connect with us

News

Masana Taurari Sun Gano Wani Tauraro Mai Launin Kore

Published

on

green star

Masana taurari sun bayyana cewa sun gano wani tauraro da ke bayyana da launin kore, lamarin da ake ganin zai iya zama sabon abin mamaki a fannin binciken sararin samaniya.

Tauraron, mai suna WD J1330+6435, yana da nisan kimanin shekarun haske 280 daga Duniya. Wani farin tauraro ne da ya rage bayan wani tauraro mai girman gaske, wanda a da yake kama da Rana, ya kai ƙarshen rayuwarsa.

Kotu Ta Yi Watsi Da Karar El-rufai Ta Neman Diyyar Naira Miliyan 120 Kan DSS, EFCC Da ICPC

Ana kiran irin waɗannan ragowar taurari da white dwarfs, wato fararen taurari da suka rage bayan tauraro ya yi amfani da yawancin makamashinsa.

Masana na zargin cewa launin koren tauraron na iya kasancewa da alaƙa da sinadaran da suka taru a cikinsa bayan ya tsotse tarkacen duwatsu daga tsohon tsarin duniyoyin da suka kasance a kewaye da shi.

A bisa bayanan kimiyya, taurari kan bayyana da launuka daban-daban, ciki har da fari, shuɗi da ruwan lemu, gwargwadon yanayin zafinsu da wasu siffofinsu.

Advertisement

An wallafa sakamakon binciken a mujallar kimiyya ta RAS Techniques and Instruments a ranar 15 ga Oktoba, 2026.

Binciken na iya ƙara faɗaɗa fahimtar masana game da sinadaran da ke cikin ragowar taurari da kuma yadda tsarin duniyoyin da ke kewaye da su ke sauyawa bayan ƙarshen rayuwar tauraro.

 

Fox2

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending