News
Wani Jami’an Dansanda Ya Kashe Abokiyar Aikinsa Kuma Ya Kashe Kansa A Kogi
Rundunar ‘Yansanda a Jihar Kogi da ke arewacin Nijeriya ta ce ta soma bincike kan wani lamari na harbe-harbe da ya faru a sansanin ASCO da ke Ajaokuta, wanda ya yi sanadin mutuwar jami’an ‘yansanda biyu a ranar Juma’ar da ta gabata. Kwamishinan ‘Yansanda, Naziru Bello Kankarofi, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, ASP Saliu Oyiza Afusat, ta fitar a ranar Lahadi.
An bayyana sunayen jami’an ‘yansandan: Kofur Amos Yusuf da kuma Kofur Grace Onimisi, waɗanda duka biyun ke aiki a Hedkwatar ‘Yansanda ta Shiyya da ke Ajaokuta.
Dakarun Sojin Sama Sun Yi Amfani Da Kusan Litar Man Jirgi Miliyan 10 Wajen Gudanar Da Ayyukan Tsaro
A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9 na dare a rukunin gidajen kwanan jami’an da ke Ajaokuta.
Binciken farko ya nuna cewa Amos, wanda ya riga ya kama aikin dare, ya bar gurin aikinsa tare da bindigarsa ta aiki kirar AK-47 inda ya nufi gidan Grace.
Ana zarginsa da buɗe mata wuta, inda ya yi mata raunuka da harsashi a ƙafa da kafaɗa da kuma ciki, sannan ya harbe kansa da bindigar.
-
News6 days ago
Matasa A Unguwar Gama Sun Yi Kira Ga Majalisar Dokokin Kano Ta Ladabtar Da Ɗan Majalisar Nassarawa Kan Zargin Cin Zarafin Gwamna
-
News6 days ago
Shugaba Tinubu Ya Ce Ba Zai Dawo Da Tallafin Man Fetur Ba Kuma Ba Ya Da-na-sanin Cire Shi
-
News5 days ago
DSS Ta Gurfanar Da Mutum Biyar Gaban Kotu Bisa Zarginsu Da Garkuwa Da ‘Yan NYSC 20 A Imo

