Connect with us

News

Kotu Ta Yanke Wa Sojoji 66 Hukuncin Kisa Saboda ‘Ja Da Baya A Fagen Daga’

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Wata kotun soji a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DR Congo) ta yanke wa sojoji 66 hukuncin kisa, bayan samun su da laifuka uku, ciki har da nuna tsoro a fagen daga, kamar yadda kafafen yaɗa labaran ƙasar suka rawaito a ranar Lahadi.

Shari’ar da aka gudanar a Kotun Sojoji ta Goma da ke lardin Arewacin Kivu, ta shafi sojoji sama da 70. An wanke sojoji huɗu daga zargin da ake musu, yayin da aka yanke wa wani soja hukuncin ɗaurin shekaru 10 a gidan yari, kamar yadda gidan rediyon Majalisar Ɗinkin Duniya, Radio Okapi, ya bayyana.

NDLEA Ta Kama Wata ‘Yar Kasar Uganda Da Ta Boye Koken Dauri 87 A Cikin wandonta

Rahoton ya ce kotun ta yanke hukuncin ne bayan ta samu waɗanda ake tuhuma da laifukan tayar da ƙayar baya, ƙin bin umarnin shugabanni da kuma nuna tsoro yayin fuskantar abokan gaba.

Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda aka samu da laifin, waɗanda ke cikin runduna ta 3415 ta sojojin ƙasar Kongo, an kama su ne a ranar 20 ga Oktoba a yankin Walikale, inda ake zargin sun aikata waɗannan laifuka.

Rundunar sojin ƙasar ta bayyana cewa ɗaya daga cikin manufofin shari’ar ita ce ƙarfafa ladabtarwa da bin ƙa’ida a cikin rundunar sojin, musamman a daidai lokacin da ake fuskantar matsalar tsaro a gabashin ƙasar Kongo.

Advertisement

A watan Oktoba, wata kotun soji a Kongo ta yanke wa wasu sojojin ƙasar 27 hukuncin kisa bisa zargin nuna tsoro, bayan sun janye daga sahun gaba na yaƙi da ‘yan tawayen AFC/M23.

An gudanar da wannan shari’a ne a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza faɗace-faɗace a gabashin ƙasar Kongo tsakanin ƙungiyar ‘yan tawaye ta Front for the Refoundation of the Nation (FRN), wadda ƙungiyar M23 ke cikinta, da kuma dakarun gwamnatin ƙasar, kamar yadda majiyoyin cikin gida suka bayyana.

 

 

TRT AFRIKA 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending