Connect with us

News

Kotu Ta Wanke Mutumin Da Ake Zargi Da Kashe Matarsa A Kano Bayan Shekaru Biyar

Published

on

kotu 768x390 (1)
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Wata Babbar Kotu a Jihar Kano ta wanke tare da sallamar Yusuf Nadabo Kawule, wanda aka gurfanar bisa zargin kashe matarsa a shekarar 2021.

Mai shari’a Nasir Saminu ne ya yanke hukuncin a Kotun Ɗaukaka Ƙara mai lamba 11 da ke Bompai, bayan kotun ta gano cewa masu gabatar da ƙara sun kasa gabatar da isassun hujjojin da za su tabbatar da zargin kisan kai.

Wasu Bata Gari Sun Kwance Fanka 25 A Wani Masallaci A Kano

An gurfanar da Yusuf ne bisa sashe na 221 na dokar Penal Code kan zargin kisan kai, amma ya musanta aikata laifin.

A yayin shari’ar, masu gabatar da ƙara sun gabatar da shaidu, yayin da wanda ake tuhuma shi ma ya gabatar da bayanansa domin kare kansa.

Lamarin da ya kai ga gurfanar da shi ya faru ne a shekarar 2021 a ƙauyen Kogo da ke Ƙaramar Hukumar Takai ta Jihar Kano.

Advertisement

Rahotanni sun nuna cewa ana zargin Yusuf ya ɗauki matarsa a kan babur domin neman gidan da za ta zauna a wani ƙauye, amma sun yi hatsari a hanya, wanda ya yi sanadin mutuwar matar.

Bayan faruwar lamarin ne jami’an tsaro suka kama shi, daga bisani aka gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin kisan kai.

Sai dai kotun ta yanke cewa masu gabatar da ƙara ba su tabbatar da zargin da ake yi wa Yusuf ba, don haka ta wanke shi tare da sallamarsa.

 

DAILY POST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending