Connect with us

News

Kwankwaso ya sayi fom ɗin N30m don tsaya wa takarar shugaban ƙasa a NNPP

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

 

Tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya biya naira miliyan 30 domin sayen fom na ‘yan takarar mukamin shugaban ƙasa a jiya Talata a ofishin jam’iyyar NNPP da ke Abuja.

Jaridar Vanguard ta ce shugaban jam’iyyar NNPP ta kasa, Farfesa Rufai Alkali tare da babban jami’in tsare-tsare Suleiman Hunkuyi ne suka tarbi tsohon sanatan.

Advertisement

Yayin da yake jawabi jim kadan bayan ya karbi fom din, ya ce jam’iyya mai mulkin Najeriya ta APC da babbar jam’iyyar adawa ta PDP ba su da sauran rawa da za su taka domin ‘yan Najeriya sun gwada su amma sun gaza.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending