News
Waɗanda ba Musulmi ba sun taya Musulmai azumin Ramadan a Saudiyya
Daga Kabiru basiru fulatan
Waɗanda ba Musulmi mazauna Saudiyya sun taya Musulmai yin azumin watan Ramadan da nufin ƙara kusanci da abota tsakaninsu da Musulmai.
Sun ɗauki azumi tare da kiyaye dokokinsa da kuma shan ruwa tare da abokanansu Musulmi a Saudiyya, kamar yadda jaridar Arab News ta wallafa a shafinta na intanet.
Ta ambato ɗaya daga cikinsu yana cewa: “Bai kamata ku yi Ramadan ku ƙadai ba – Wannan lokaci ne na ƙarfafa abokantaka da karimci.”
Wasu daga cikinsu sun ce Azumi ya ƙara masu kusanci da abokansu Musulmi.
A cewar jaridar, duk da cewa akwai bambancin addini, amma ƴan ƙasashen waje waɗanda ba Musulmi na ƙara rungumar al’adun Saudiyya..
Baya ga kasancewar Ramadan watan Ibadah da tasirinsa ga ƙara kusantuwa ga Allah, bincike ya nuna yin azumi na kaucewa ci da sha daga fitowar al fijr zuwa faɗuwar rana yana da fa’ida wajen inganta lafiyar ɗan adam.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
