Connect with us

News

Antonio Guterres zai gana da shugaba Buhari na Najeriya

Published

on

Daga yasir sani abdullahi

 

 

A yau ne ake sa ran babban sakatare janar na Majalasar Dinkin Duniya ,Antonio Guterres, zai gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a yayin ziyarar da ya kai kasar.

Babban jami’in Majalisar Dinkin Duniyar, sai da ya fara kai ziyara Maiduguri, babban birnin jihar Borno inda ya gana da Gwamna Babagana Umara Zulum, da kuma iyalan mutanen da rikicin Boko Haram ya yi sanadin rasa rayukansu.

Fadar gwamnatin Najeriya dai ta bakin mai magana da yawun shugaba Buharin Malam Garba Shehu, ta shaida wa BBC cewa, suna maraba da wannan ziyara ta Antonio Guterres.

Malam Garba Shehu, ya ce sai babban jami’in ya isa fadar gwamnatin Najeriyar sannan zai yi bayani a kan abin da kawo shi, domin su basu san dame ya zo ba.

Advertisement

Ya ce “Kunnenmu a bude yake idan yazo sun gana da shugaba Buhari kamar yadda aka tsara, sannan ya yi bayani a kan gudunmuwa ko kuma karin gudunmuwar da Majalisar Dinkin Duniya take ganin za ta ba wa Najeriya a kan halin da take ciki na matsalar tsaro.”

Malam Garba Shehu ya ce ba mamaki baya ga gudunmuwa, jami’in zai iya janyo hankalin kasashen duniya masu arziki su zo su ba da na su tallafin, saboda gwamnatin tarayya ita kadai ba za ta iya ba, bisa la’akari da yadda matsalar tsrao ta jefa yankuna da dama na Najeriya cikin ƙunci.

Ana sa ran sakatare janar din zai kuma gana da shugabannin addinai da na kungiyoyin mata da matasa da kuma shugabanin kamfanoni masu zaman kansu.

Baya ga wadannan mutane da zai gana da su, zai kuma gana da jami’an difilomasiyya da ma wadanda ke sansanonin ƴan gudun hijra a jihar Borno.

Kafin ya kai ziyara Najeriya, sai da ya je Jamhuriyar Nijar ya gana da shugaban kasar Muhammed Bazoum, in da har ya yaba da irin kokarin da jami’an tsaron kasar ke yi wajen yaki da masu tayar da kayar baya.

Kazalika, ya yi kira ga kasashen duniya su taimaka wa sojojin Jamhuriyar Nijar ɗin domin yaki da masu tayar da kayar baya da suke yawan kai hare-hare a kasar.

Advertisement

A yayin da jawabi lokacin ziyararsa a Niamey babban birnin kasar, babban jami’in na Majalisar Dinkin Duniya ya ce rikicin da ke faruwa a yankin Sahel ya zama babbar barazana ga duniya.

Antonio Guterres ya kara da cewa Jamhuriyar Nijar ba za ta iya tunkarar matsalar masu ikirarin jihadi ita kadai ba kuma ya yi kira ga wasu kasashe su taimaka mata da horaswa da kuma kayan yaki.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending