News
EFCC ta kama Akanta Janar na Najeriya Ahmed Idris
Daga yasir sani Abdullah
Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta kama Akanta Janar na Najeriya bisa zarginsa da almundahana ta naira biliyan 80.
Hukumar ce ta bayyana haka a shafinta na Facebook inda ta ce ta kama shi a ranar Litinin 16 ga watan Mayun 2022.
Hukumar na zargin Ahmed da karkatar da kuɗin ta hanyar amfani da abokansa da iyalai da sauran hanyoyi.
EFCC ta ce an yi amfani da kuɗin wurin gina rukunin gidaje a Kano da Abuja.
An kama Idris bayan ya ƙi karɓar gayyatar da EFCC ta rinƙa aika masa domin tuhumarsa kan zarge-zargen da ake yi masa, kamar yadda hukumar ta bayyana.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
