News
Ganduje ya daƙile ficewar Barau daga APC ya kuma bar masa takarar Sanata
Daga kabiru basiru fulatan
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya janye takarar sa ta Sanata bayan sulhu da su ka yi da Barau Jibrin, Sanatan Kano ta Kudu.
Rahotanni sun baiyana cewa Barau Jibrin ya gana da shugabannin jam’iyar NNPP a kwanan nan domin sauya sheƙa zuwa jam’iyar daga APC.
Tun da fari, Jibrin ya bi tsohon gwamna, Ibrahim Shekarau su ka kafa wani tsagin na APC mai suna G-7.
Akalla mutum 32 ne ‘yan bindiga suka kashe daga ranar 8 zuwa 14 ga Mayu a Najeriya
A kwanan nan ne Ganduje ya sayi fom ɗin takarar Sanatan Kano ta Arewa domin ya maye gurbin Barau, wanda shi ka ya sayi fom ɗin duk da cewa bai bar APC ba.
Sai dai kuma majiyar mu ta baiyana cewa tuni Ganduje da Barau su ka sasanta, inda tuni ma gwamnan ya janye wa Sanatan takarar.
Sakataren jam’iyar APC a Kano, Zakari Sarina, ya tabbatar da batun ga manema labarai a jiya Litinin.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
