News
MINISTOCIN BUHARI SUN SAKE SHAWARAR AJE MUKAMANSU.
Daga Khadija Abdullahi Mahmud.
Wasu daga cikin ministocin gwamnatin Najeriya da suka sayi fom domin tsayawa takarar zabe da kuma ban kwana da majalisar ministoci a makon jiya, sun koma bakin aikin su inda suka sanar da janyewa daga shirin tsayawa zaben mai zuwa duk biyan makudan kudade wajen sayen fom.
A makon jiya ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya baiwa wadannan ministoci umurnin aje aikin su kafin ranar 16 ga watan nan da kuma yi musu walimar ban kwana saboda bayyana aniyar su ta tsayawa zabe.
Sai dai tuni wasu daga cikin su suka sake ra’ayi dangane da tsayawa zaben, inda suka bayyana cewar bayan tuntuba daga aminan su, sun yanke hukuncin janye takarar da kuma ci gaba da rike kujerun su a matsayin ministoci.
Daga cikin irin wadannan ministoci akwai Timipriye Sylva, karamin ministan albarkatun man fetur da ya biya naira miliyan 100 domin tsayawa takarar shugaban kasa da ministan shari’a Abubakar Malami da ya sayi fom na tsayawa takarar gwamnan Kebbi akan naira miliyan 50 da Paulime Tallen, ministar kula da harkokin mata da ta sayi fom domin tsayawa takarar Sanata.
Sylva yace bayan tattaunawa da na kusa da shi da kuma lura da irin dimbin aikin dake ma’aikatar sa ya janye daga shirin tsayawa takarar zaben shugaban kasar.
Ita ma Pauline Tallen tace ta janye ne domin ci gaba da gini akan gishikin samun daidaito tsakanin jinsi a matakan shugabancin Najeriya, yayin da ta godewa dimbin magoya bayan ta.
Tun a makon jiya Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emiefele yace ya janye daga takarar tsayawa shugaban kasar bayan wasu magoya bayan sa sun biya naira miliyan 100 domin saya masa fom.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
