Connect with us

News

Yadda gwamnatin Lagos ta jefa ‘yan kasuwar dabbobi ta Alaba Rago cikin zulumi

Published

on

Yan kasuwa a babbar kasuwar dabbobi ta Alaba Rago da ke birnin Lagos na Kudancin Najeriya sun shiga zulumi bayan da gwamnatin Jihar ta ba su wa’adin kwanaki 14 su fice daga cikinta.

Gwamnatin Jihar ta ce za ta dauki matakin ne domin samun damar inganta kasuwar da fasali irin na zamani.

Rundunar ‘yan-sandan Jihar ta bayyana cewa sanarwar korar ‘yan kasuwar daga Alaba Rago ta fito ne bayan tattaunawar da gwamnatin Jihar ta yi da wakilan ‘yan kasuwar.

Ta kara da cewa ana samun matsalolin rashin tsaro da ke faruwa a kasuwar da ma yankin.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending