Daga yasir sani abdullahi
Wata kotu a birnin Lagos a Najeriya ta yankewa wani dan kasar Denmark hukuncin kisa.
Babbar kotun ta Legas ta kama mutumin mai shekara 53 da laifin kisan matarsa Zainab ‘yar Najeriya, da ‘yarsu mai shekara uku da ake kira Petra a wani rikicin iyali.
Shekaru hudu kenan ana ta fadi tashigaban shari’a kafin yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar Juma’a.
Gwamnatin Legas ce ta shigar da ƙara tana zargin Peter Nielsen da laifin kisan matarsa da ƴarsa kuma Mai Shari’a Bolanle Okikiolu-Ighile ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Sai dai ba kasafai ake aiwatar da hukuncin kisa a Najeriya ba saboda matsalolin kare haƙƙin bil’adama, kuma duk da cewa har yanzu kotuna na yanke hukuncin yawanci mutum kan kare rayuwarsa ne a tsare
