Connect with us

News

BAYAN FILLE KAN DAN MAJALISA DA KUMA SACE WANI DAN SIYASA YAN BINDIGA SUNCE ZASU DAWO.

Published

on

 Daga Khadija Abdullahi Mahmud.

 

Wadanda ake zargi da hannu wajen kashe Okechukwu Okoye sun yi barazanar cigaba da yin ta’adi
A karshen makon da ya wuce ne aka tsinci kan ‘dan majalisar Aguata II, Hon, Okechukwu Okoye
Mutanen gari sun tsinci wata takarda da ta ce ‘yan bindigan za su cigaba da kashe ‘yan majalisa
Daily Trust ta rahoto cewa miyagun ‘yan bindigan da ake zargi da laifin kashe Hon. Okechukwu Okoye, sun ce za su cigaba da kashe wasu ‘yan majalisan.

An raba takalmin zinare tsakanin Mohamed Salah da Son Heung-min

Wani mazaunin garin Nnobi ya shaidawa jaridar cewa wadanda suka yi wannan danyen aiki sun bar wata takardar barazana a gefen kan da suka jefar a titi.

Sahara Reporters ta bayyana cewa takardar da aka bari dauke da kan da aka datse ta na barazanar mutanen za su cigaba da kashe ire-iren Hon. Okoye.

Advertisement

“A takardar, makasan sun yi alkawarin cewa za a zubar da wasu kawunan. Ba a fahimci abin da takardar da kunsa sosai ba.”
A cikin takardar, an rubuta cewa, ‘duk inda ku ka je, ba za ku iya boyewa a ko ina ba. Za mu bi ku duk daya bayan daya…”
“…Domin jami’an ‘yan sanda da dakarun sojojin kasa ba matsalar mu ba ne kuma a yanzu.”

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending