News
AN SHIGA RUDANI; WASU SUN `SACE´ MASU KADA KURI´A A WAJEN ZABEN YAN TAKARAR PDP.
Daga Khadija Abdullahi Mahmud.
Rikici ya kaure tsakanin magoya bayan wasu ‘yan takaran PDP a karamar hukumar Gbako a Neja
A jihar Ogun, ana rade-radin an dauke wadanda za su zabi ‘yan takarar majalisar wakilan tarayya
A wani rahoto da ya fito daga Daily Trust, an ji cewa wasu sun samu rauni wajen zaben fitar da gwanin da ake kokarin yi a Lemu, garin Gbako, jihar Neja.
Ba a iya karasa zaben fitar da gwani a kauyen Lemu ba a dalilin rikici da aka samu tsakanin magoya bayan Alhaji Gimba Tswatagi da na Nma Busokun.
Rahoton da mu ka samu ya ce an tsaida zaben bayan magoya bayan ‘yan takarar sun aukawa junansu da makamai, a karshe dai malamin zabe ya tsere.
Abin farin cikin shi ne PDP ta gudanar da zabe lafiya kalau a wasu garuruwan na Neja irinsu Lavun, Edati, Mokwa, Shiroro, Chanchaga, Bosso, da Gurara.
Malamin zaben da PDP ta tura, Abimbola Ademuyiwa tabbatar da cewa an samu sabani wajen zaben, hakan ya jawo wankin hula ya kai wa jam’iyyar PDP dare.
Sai bayan karfe 8:00 aka fara shirin kada kuri’ar tsaida ‘yan takarar ‘dan majalisa. Rotimi George Taylor mai neman tikiti ya tabbatar da zargin satar masu yin zabe.
Mbappe ya yi alkawarin zama babban mai goyon bayan Real Madrid
Taylor ya shaidawa ‘yan jarida an yi garkuwa da wasu daga cikin masu kada kuri’a a zaben da nufin a tursasa su wajen tsaida ‘dan takarar majalisa da karfin tsiya.
Amma Sakataren PDP na Ogun, Sunday Solarin ya musanya zargin sace masu kada kuri’a. Mista Solarin ya ce an canza wurin yin zaben ne saboda matsalar tsaro.
The Nation ta ce haka abin ya faru a yankunan Akwa Ibom Bayelsa da Ondo da jihar Delta. A Edo kan ‘Yan PDP ya rabu biyu, yayin da aka daga zabukan Imo da Filato.
