Connect with us

News

Gwamna Masari zai kashe Naira miliyan 100 don gyara kauyen Shinfida saboda barnar da ‘yan bindiga sukai

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin 

 

 

 

Gwamna Aminu Masari ya ce gwamnatinsa ta ware Naira miliyan 100 domin gyara kauyen Shinfida da ‘yan fashin suka bata a karamar hukumar Jibia a jihar.

“A halin yanzu, muna kashe sama da Naira miliyan 100 don gyara kauyen Shinfida, wanda ‘yan bindiga suka kora suka kona su, wadanda suka tilasta wa mutane 13,500 komawa jamhuriyar Nijar,” Mista Masari ya ce yayin da yake mayar da martani ga Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti da ya je Katsina domin burinsa na shugaban kasa.

Advertisement

AN SHIGA RUDANI; WASU SUN `SACE´ MASU KADA KURI´A A WAJEN ZABEN YAN TAKARAR PDP.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin sa ta aika da abinci ga iyalan wadanda abin ya shafa, ya kara da cewa sojoji sun dawo Shinfida.

“Lokacin da mutanen Shinfida suka fita, ‘yan bindigar sun kona kauyen tare da lalata komai.

“Mahimmanci a gare mu shi ne tsaro da gyara wadannan kauyuka da al’ummomin, maido da tsarin rayuwarsu da samar da ilimi na asali,” in ji shi.

Ya kara da cewa duk da cewa wasu ‘yan gudun hijirar sun fara komawa cikin al’umma, amma da yawa har yanzu ‘yan gudun hijira ne a makwabtan jamhuriyar Nijar.

Masari ya ce babban abin da ke da matukar muhimmanci kuma cikin gaggawa a jihar shi ne farfado da tattalin arzikin yankunan karkara na wadanda abin ya shafa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending