Hukumar da ke kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce adadin waɗanda yaƙi a Ukraine da sauran musibu a kasashen duniya suka sa suka bar gidajensu sun kai mutum miliyan 100.
Hukumar ta ce wannan ne karon farko a tarihi da aka taba samun wannan adadi. Kutsen Rasha a Ukraine kawai ya raba mutum miliyan takwas da gidajensu, yayin da wasu, miliyan shida suka bar kasar kwata-kwata.
A bara ne Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin ya kai mutum miliyan 90, a dalilin rikici a kasashen Habasha da Burkina Faso da Myanmar da Najeriya da Afghanistan da kuma Jamhuriyar Dimokraɗiyar Kongo.
