News
Kwankwaso ne mabuɗin samun nasara a babban zaɓen 2023 – Reno Omokri, jigon PDP
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Wani Jljigo a babbar jam’iyyar adawa ta PDP kuma na hannun daman tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, Reno Omokri ya bayyana cewa, tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, shi ne mabuɗin cin zaben shekarar 2023 kuma idan har PDP na bukatar samun nasara sai ta hada kai da jagoran na NNPP.
Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso dai shi ne dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP wacce ke mamayar magoya baya mussaman a yankin Arewacin Najeriya, da ake ta kaura daga jam’iyyun APC da PDP zuwa cikinta.
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Reno Omokri ya bayyana cewa, Kwankwaso zai samu tarin kuri’u a yankin Arewa maso yamma.
“Yakamata PDP ta kulla alaka da Kwankwaso. Saboda idan Kwankwaso ya tsaya takara ba zai nasara ba. Kodayake, zai samu tarin kuri’u a yankin Arewa Maso yamma”.
Jigo a PDPn yayi gargadin cewa idan jam’iyyar tayi wasa Kwankwaso zai kawo matsala wanda hakan zai sa APC ta samu nasara.
” Kwankwaso mabudi ne! Mun sani ba zai ci zabe ba amma tabbas zai hana PDP samun nasara.”
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
