Connect with us

News

Dan takarar PDP ya bukaci Daliget su dawo masa da kudinsa bayan yasha kaye

Published

on

 

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

Adam Namadi, dan gidan tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, ya bukaci masu zaben dan takara a zaben cikin gida na jam’iyya (Daliget) na jam’iyyar PDP cewa su dawo masa da kudin Naira Miliyan biyu kowannesu da ya basu kafin fara zaben fidda gwani na yan takarar majalisar wakilai a yankin Kaduna ta Arewa.

Daliget sun samu Miliyoyin Nairori daga hannun masu neman tikitin takara da suke yunwar samun mulki, ciki harda dan majalisa mai ci, Samaila Suleiman, wanda ya baiwa Daliget tsakanin Miliyan uku da rabi zuwa Miliyan hudu, kuma shi ne yayi nasara a zaben da kuri’u 22.

Suleiman dai ya fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP babu jimawa, sannan ya tsaya takara kuma ya doke abokan karawarsa, Usman ABG da kuma shi Adam Namadi, dan gidan tsohon mataimakin shugaban kasar Nigeria, Namadi Sambo.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending