News
A karo na gaba, kotu ta sake tabbatar da Sagagi a matsayin shugaban PDP na Kano
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Babbar kotun tarayya dake zamanta a Kano, ta tabbatar da Shehu Wada Sagagi a matsayin halattaccen shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kano, biyo bayan karar da wani mai suna Bello Gambo Bichi ya shigar yana zargin Sagagi da alakar siyasa tsakaninsa da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya fice daga jam’iyyar zuwa NNPP mai kayan marmari.
Idan baku manta ba, a ranar 17 ga watan Mayun da muke ciki, mai shari’a A.M Liman ya dakatar da shugabancin Sagagi da cigaba da jagorantar duk abinda ya shafi jam’iyyar, to sai dai yau kuma kotun ta amince da Sagagin a matsayin shugaba.
Yayin zaman shari’ar, kotun tace, mai kara, Gambo Bichi, ya gaza tabbatar da hujjojin da zasu gamsar da kotun kan abinda yake zargi, kuma baya cikin zababbu a jam’iyyar, a saboda aka dage cigaba da zaman shari’ar har zuwa ranar 26 domin cigaba da zama.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
