News
YANZU-YANZU: Peter Obi, ya yi Allah wadai da Ka-she musulmai ‘yan Arewa a Anambra
Daga khadija Abdullah muhmd
Dan takarar shugabancin Najeriya, Peter Obi, wanda ake sa ran Kwankwaso zai tsayar a matsayin mataimakinsa a zaben 2023, ya bayyana damuwarsa kan yadda ake
Ka-she mutane haka kawai a kudancin kasar nan.
Obi ya bayyana hake a shafin sa na Twitter.
“Na damu matuka da yadda Ka-she Ka-she ke kara ta’azzara a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, musamman Ka-she wata mata mai juna biyu da ‘ya’yanta hudu a jihar Anambra da kuma yadda aka Fi-lle kan wani dan majalisar dokokin jihar kwanan nan.” Inji wallafar
“Iyalan wadanda suka mutu sun cancanci a yi musu adalci, kuma za a iya yin hakan ne kawai idan aka kama wadanda suka aikata wadannan munanan ayyuka kuma su fuskanci fushin doka. Lallai ina kira ga hukumomin tsaro da su tabbatar da wannan da sauran abubuwan da suka shafi bin doka da oda.”
“Ina mika sakon ta’aziyyata ga iyalan marigayin tare da yin kira ga masu ruwa da tsaki da suka hada da al’ummomin da abin ya shafa da hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya da gwamnati a dukkan matakai da su hada kai domin dawo da zaman lafiya da aka taba samu a baya.”
“Gwamnati a nata bangaren dole ne ta sauke nauyin da ke kanta na kare al’ummarta.”
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
