Connect with us

News

Shugaba Buhari ga ‘Yan Siyasa – Kada ku yi amfani da sunana ku zalunci al’ummar ku lokacin zabe

Published

on

Khadija Abdullahi Mahmud 

 

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi ‘yan siyasa akan kada suyi karya da sunan shi wajen neman mulki a mazabunsu..

Jam’iyyar APC Ta Dage Zaben Fidda Gwani Na ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a ranar Alhamis 22 ga watan Yuli, a lokacin da ya karbi gwamnonin jam’iyyar APC da suka kai masa ziyarar barka da Sallah a gidan shi dake Daura, cikin jihar Katsina.

Advertisement

A cewar jaridar Nigerian Tribune, shugaba Buhari ya bukaci masana tarihi da su zama masu gaskiya wajen adana bayanan ayyukan da gwamnatinsa tayi, musamman ma wajen taimakawa masu jefa kuri’a su zabi shugaba na gari.

A wata sanarwa da babban mai taimakawa shugaban kasar na musamman a fannin yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar, shugaba Buhari ya bayyana cewa makomar Najeriya za ta kasance ne idan har an nuna kwazo da gaskiya, musamman ma ga wadanda suke rubuta bayanai na tarihi, da kuma yin nazari akan yanayi da ake ciki, haka kuma da sanin darajar abin da ya faru da kuma wanda zai biyo baya.

Shugaba Buhari ya ce zai zama abin takaici, idan har ‘yan siyasa zasu yaudari mutane ta hanyar yi musu karairayi, da nuna son kai, ya kuma nuna bukatar sanya Najeriya a farko kafin kowanne abu.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending