News
Buhari ya roƙi ‘yan Najeriya ‘kada ku ƙyale PDP ta mayar da Najeriya baya’.
Daga khadija Abdullahi muhmd
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya su tabbata ba su bar jam’iyyar adawa ta PDP “ta mayar da ƙasa baya ba”.
Ina Makomar Sha’aban Ibrahim Sharada A Siyasar Kano?
Da yake jawabi a wurin zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyarsu ta APC, Buhari ya ce APC ta sauya Najeriya ta hanyar gudanar da ayyukan raya ƙasa.
“Wajibi ne mu zaɓi masu adalci ‘yan kishin ƙasa da ke da aƙidar haɗa kan ƙasarmu…don ciyar da ita gaba.
“Bai kamata mu ƙyale PDP ta mayar da Najeriya baya ba.”
Zuwa lokacin haɗa wannan rahoton PDP ba ta mayar da martani ba, wadda tuni ta zaɓi Atiku Abubakar a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a babban zaɓe na 2023.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
