News
Mutum Guda Ya Mutu A Filato, Yan sanda Sun Karyata Kai Hari A Kwalejin Kimiyya
Daga kabiru basiru fulatan
Rahotanni sun ce an kai harin ne a tashar ta Emmy daura da cocin Assemblies of God’s Church da ke kusa da makarantar da misalin karfe 10:45 na dare.
Shugaban EFCC Ya Bayyana Hanya Mafi Sauki Da Barayin Gwamnati Ke Boye Kudadensu a Najeriya
Rundunar ‘yan sandan jihar Filato a ranar Asabar ta tabbatar da kashe mutum daya a hanyar Mararaban Jama’a Uwa Riyom a karamar hukumar Riyom ta jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Alabo Alfred, yayin da yake tabbatar da afkuwar lamarin, ya karyata rahotannin da ke cewa wasu ‘yan ta’adda sun kai hari a makarantar gwamnati da ke Kuru, na garin Jos a daren Juma’a.
Rahotanni sun ce an kai harin ne a tashar ta Emmy daura da cocin Assemblies of God’s Church da ke kusa da makarantar da misalin karfe 10:45 na dare.
Amma rundunar ‘yan sandan ta ce, “Rundunar ‘yan sandan ta na Sami bayanan ne a ranar 10/06/2022 da misalin karfe 2000 na safe, an samu labarin wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suna harbe-harbe a Mararaban Jama’a, Riyom road ba kusa Science School Kuru Jos ba. Sashin yada labarai ne na rundunar suka ruwaito shi.
“Bayan samun rahoton, wata babbar tawaga ta ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro suka kai dauki cikin gaggawa zuwa wurin da lamarin ya faru, amma da isa wurin, ‘yan bindigar sun gudu sun bar mutum daya ya mutu, uku kuma suka jikkata. An kai wadanda suka jikkata nan take asibiti domin yi musu magani. A halin yanzu dai ‘yan sanda suna kan bin wadanda ake zargin da suka tsere,” in ji ‘yan sandan.
DSP Alfred ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Bartholomew N. Onyeka, ya shawarci jama’a da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau a kullun domin kuwa tuni an dawo da zaman lafiya a yankin, yana mai ba da tabbacin cewa mutanensa suna nan a wurin domin dakile duk wani rikici da ya barkewa.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
