Business
Gwamnati Za Ta Kafa Kamfanin Sarrafa Nama A Yobe
Daga Maryam bashir musa
Gwamnatin Jihar Yobe tare da hadin gwiwar wani kamfanin kasar Masar sun kammala shiri tsaf domin kafa kamfanin sarrafa nama a Damaturu, babban birnin Jihar.
Hukumar NDLEA ta gargaɗi maniyyatan Aikin Hajji
Hukumar gudanarwar kamfanin mai suna Messrs Los Amigos, ta ziyarci Gwamnan Jihar, Mai Mala Buni, a wani bangare na matakan karfafa yarjejeniyar kafa sabon kamfanin a Jihar. Kwamishinan Kasuwanci na Jihar, Alhaji Barma Shettima ne ya jagoranci Majalisar Zartarwar Jihar, yayin da Injiniya Halal M. El-Ghor, ya jagoranci abokan hadin gwiwar kasar Masar wajen yi wa mai girma Gwamnan Jihar cikakken bayani kan aikin.
Tawagar ta yi wa Gwamna bayani kan manufar aikin, da yadda zai samar da kudade ga gwamnati da yadda jadawalin aiwatar da shi zai kasance, tasirinsa ga tattalin arziki da kuma bunkasa sana’ar kiwon dabbobi a jihar.
Gwamna Buni ya bayyana kwarin gwiwar cewa aikin zai habaka tattalin arzikin jihar da na al’ummarta.
Ya yi nuni da cewa Jihar Yobe tana da dabarun kiwon dabbobi masu yawa don samar da nama mai inganci zuwa kasuwannin cikin gida da kuma fitar da su zuwa kasashen waje.
Buni ya bukaci ’yan kwamitin da su mayar da hankali tare da tabbatar da aiwatar da tsari mai kyau don yanayin ya kai ga nasara.
A cikin kwamatin gudanarwar dai akwai Shugaban Ma’aikata Fadar Gwamnatin Jihar, Alhaji Abdullahi Yusuf Gashua da Babban Sakataren Gidan Gwamnatin Jihar, Alhaji Liman Ibrahim da Dokta Idrissa Madaki da Alhaji Hamza Saidu. Source (daiy trust)
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
