Connect with us

News

Ƴan ci ranin Afrika 18 sun rasu a hanyar zuwa Sifaniya

Published

on

Muhammad Muhammad zahraddin

Hukumomi a Moroko sun ce ‘yan ciranin Afrika 18 ne suka mutu, lokacin da suka yi kokarin tsallakawa yankin Melilla na Sifaniya a jiya juma’a.

Advertisement

Jami’ai sun ce yawanci sun faɗo ne daga doguwar katangar iyakar, wasu sun mutu ne lokacin da suka ui kokarin tserewa jami’an tsaron haɗin gwiwa tsakanin Moroko da Sifaniya.

Dama can ƴan Afrika na amfani da yankin Melilla na Sifaniya a matsayin hanyar isa Turai, a ranar juma’a kusan ƴan cirani 2000 ne suka yi ƙoƙarin tsallaka iyakar a jiya Juma’a.

Advertisement

Firaiministan Sifaniya Pedro Sanchez, ya ce jami’an tsaro sun yi maganin masu tayar da zaune tsaye a iyakarsu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending