News
Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta ce Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke kan gaba a duniya wajen noma da shan Tabar Wiwi.
Daga kabiru basiru fulatan
Shugaban hukumar, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya) ne ya bayyana hakan ranar Talata yayin bude wani taro kan kiyaye ta’ammali ga miyagun kwayoyi da hukumar ta shirya wa matan Gwamnoni a Abuja.
Tikitin Gasar Cin Kofin Duniya Na ƙarshe Za A Fara Siyarwa A Mako Mai Zuwa – FIFA
Ya ce matsalar shan kwaya na daya daga cikin manyan matsalolin da suke addabar duniya a halin yanzu.
A cewarsa, “Kadan daga cikin illolin shan kwaya shi ne kamuwa da cututtuka iri-iri da kuma mutuwa tun da kuruciya, kuma abubuwa ne da bai kamata da duk gwamnatin da ta san me take yi ba za ta zura ido a kai ba.
“Shekara hudu da suka shude, muna da mutum miliyan 10.6 da ke shan Tabar Wiwi, wanda hakan ke nuni da cewa muna cikin kasashen da ke kan gaba a wannan fagen a duniya,” inji shi.
Buba Marwa ya kuma ce Najeriya ta kuma zama tamkar kwandon shara ga miyagun kwayoyi da magunguna irin su Tramadol da Kodin, sannan ta zama cibiyar hada-hadar Hodar Iblis da Tabar Wiwi zuwa wasu kasashen.
Sai dai ya ce za a iya shawo kan matsalar idan aka rungumi nagartaccen tsarin magance matsalar, kamar irin wannan taron bitar.
