Connect with us

News

An rufe makarantar sakandire sakamakon mutuwar ɗalibi a Legas

Published

on

Babajije Sanwo Olu

 

Daga Khadija Abdullahi Mahmud

 

 

 

Ma’aikatar ilimi ta jihar Legas ta rufe makarantar framare ta Redeemers da ke garin Ogba.

Advertisement

 

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta nuna cewa an dauki matakin ne biyo bayan mutuwar wani dalibi mai shekaru biyar, wanda ake zargin ya nutse a ruwa yayin wani darasin ninkaya da ake koyarwa a makarantar.

Ƴan daba sun far wa ƴan majalisar dokokin Bauchi inda su ka jikkata 6

 

Kwamishiniyar ilimi ta jihar Folasade Adefisayo, ta shaida wa ƴan jarida cewa makaratnar za ta ci gaba da kasancewa a rufe, har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan ayyukanta.

 

Advertisement

A halin da ake ciki dai ƴan sanda na binciken lamarin.

 

Amma wani binciken farko da ofishin tabbatar da ingancin ilimi na ma’aikatar ya yi, ya nuna cewa makarantar mai suna Redeemers Nursery and Primary School ba ta kammala rajistar ta ba, don haka har yanzu ba a amince da ita ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending