News
Kada a gajiya wajen yin addu’a don samun zaman lafiya-Hamisu Ibrahim chadari.
Daga Maryam bashir musa
Shugaban majalissar dokokin Kano Injiniya Chidari, yayi kira ga al’ummar jihar nan da kada su gajiya wajen yin addu’a ga Allah S.W.T don samun mafita kan matsalar tsaron da kasar nan ke fuskanta.
Southampton Ta Sayi Dan Wasan Najeriya Joe Aribo
Shugaban majalisar dokokin ya bayyana hakane a sakonsa na barka da sallah ga al’ummar jihar Kano wanda daraktan yada labarai na majalisar dokokin Kano Uba Abdullahi ya fitar Lahadin nan.
Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ya yabawa jami’an tsaron kasar nan bisa kokarin da suke don tabbatar da doka da Oda a cikin kasar nan.
Ya kuma bayyana yin biyayya ga dokokin addinin musulunci amatsayin hanyar cigaban al’umma.
Yace biyayya ga koyarwar addinin musulunci ce hanya mai sauki ta samun cigaba.
Ya yabawa jami’an tsaron kasar nan bisa kokarin da suke don tabbatar da doka da Oda.
Shugaban majalisar ya kuma mika sakon barka da salla ga gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, da matemakinsa da mambobin majalisar zartaswa dana dokoki.
Haka zalika Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ya kuma yi fatan alheri ga sarkin Kano da Bichi da Gaya da Karaye da Rano bisa bukukuwan sallah.
Shugaban majalisar dokokin ta Kano Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ya kuma yi fatan alheri ga al’ummar Makoda da Dambatta bisa goyan bayan da suke bashi, inda ya basu tabbacin rubanya kokarin sa a majalisar wakilai ta tarayya.
