Connect with us

News

Mun mayar da kamfanin NNPC hannun ‘yan kasuwa – Buhari

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar sabon kamfanin mai na kasar wanda aka sauya wa fasali, inda a yanzu kamfanin na NNPC ya koma wani kamfanin kasuwanci mai zaman kansa

 

Advertisement

An yi kaddamarwar ne a wani kwarya-kwaryan biki da aka gudanar a Abuja babban birnin kasar .

Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Sabon Tambarin Kamfanin Mai Na Kasa NNPC

Shugaba Buhari ya fara ne da gode wa mahartar taron, wanda ya kira shi da ”mai dimbin tarihi”.

 

A jawabin da ya gabatar a wurin taron, shugaba Buhari ya ce an mayar da ikon gudanar da kamfanin ga ‘yan kasuwa ne, saboda inganta shi, don samar wa kasar makashin da take bukata.

 

Advertisement

Ya kuma kara da cewa ”daga yanzu kamfanin NNPC ya koma karkashin gudanarwar ‘yan kasuwa, zai kasance kamfani mai zaman kansa ta yadda zai yi gogayya da takwarorinsa a fadin duniya, domin ci gaba da bunkasa hannayen jari sama da miliyan 200 tare da habaka fannin makashi a fadin duniya”.

 

”A yanzu doka ta dora wa kamfanin alhakin tabbatar da samar wa Najeriya wadataccen makashin da take bukata domin samun habakar tattalin arzikin ta hanyar farfado da wasu fannonin da ke bukatar makashin”. in ji Shugaban na Najeriya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending