Connect with us

News

DA ƊUMI-ƊUMI: Sojoji sun kuɓutar da basaraken Filato sun kuma kama 8 da ga waɗanda su kai garkuwa da shi

Published

on

FB IMG 16409701719838851
Spread the love

Mai Martaba Charles Mato Dakat, basaken jihar Filato da ƴan fashin daji su ka yi garkuwa da shi, ya shaƙi iskar ƴanci.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai ƴan ta’addan su ka yi garkuwa da Dakat, wanda shine Sarkin Lardin Gindiri a Ƙaramar Hukumar Mangu, Jihar Filato da misalin ƙarfe 1 na dare.

A jiya ne dai rahotanni su ka fito cewa masu garkuwar da shi su ka tuntuɓi iyalan sa, inda su ka nemi naira miliyan 500 kuɗin fansa.

Advertisement

Amma, sai Kwamandan rundunar Sintirin Safe Haven da ke Gyanbus, Janar Ibrahim Ali ya sanya dakaru su zama cikin shirin kuɓutar da Sarkin.

Da ga bisani ne su ka kuɓutar da shi kuma su ka cafke mutum 8 da a ke zargin da su a ka ɗauke Sarkin kuma an nan a na samun bayanai da ga gare su.

Rundunar Sojin Ƙasa ta Ƙasa ta ce dakarun Safe Haven sun duƙufa wajen neman sauran da su ka aikata wannan laifin kuma ta ci alwashin sai ta kamo su an kai su kotu domin su girbe abinda su ka shuka.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *