News
Daga sama aka ƙaƙaba wa Kanawa Ganduje a 2019 – Kwankwaso
Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sake jaddada abun da ya sha faɗa a baya, cewa wasu manya ne daga sama suka tursasa wa al’ummar Kano gwamnan da yanzu yake kan mulki Abdullahi Umar Ganduje duk da cewa ya faɗi zaɓe a 2019.
Yayin wata hira ta musamman da jaridar Punch Kwankwaso ya ce ”Na tabbatar yanzu wadanda suka yi hakan suna da na sanin abun da suka yi wa Kano. Duk jama’ar Najeriya sun san cewa Ganduje ya fadi zaɓen nan, amma haka suka tursasawa mafi yawan jama’a ra’ayin wadanda ba su taka kara sun karya ba wanda shi ne babban laifin da wani zai aikata”.
Ya ƙara da cewa abun takaici ne yadda wasu tsiraru suka kasa ganin abun da talakawa suka hango wa kansu.
”Muna da ƙarin da iya hana su abun da suka so yi a wannan lokaci, amma sai muka yi la’akari da cewa idan muka biye musu hakan ba zai haifar da ɗa mai ido ba, don haka muka bar su da aniyarsu, muka bi matakin shari’a, amma a nan ma aka yi abun da aka yi” inji Kwankwaso.
A halin da ake ciki dai ana raɗe-raɗin sasantawa tsakanin tsohon gwamnan na Kano Rabiu Musa Kwankwaso da Ganduje, bayan ziyarar ta’aziyya da Gandujen ya kai wa Kwankwaso.