News
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa Bashir Tofa ya rasu
Daga Muhammad zahraddin¸
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar Najeriya a jam’iyar NRC, Alhaji Bashir Usman Tofa ya rasu.
Marigayin ya rasu da asubahin ranar Lahadi bayan wata gajeriyar rashin lafiya kamar yadda majiya daga iyalansa suka tabbatar.
Marigayin ya rasu yana da shekaru 74 a duniya.
Idan za a iya tunawa a ƙarshen makon da ya gabata ne aka fara raɗe-raɗin cewa Bashir Tofa ya rasu, wanda daga baya iyalansa suka musanta raɗe-raɗin.
Ku biyo mu domin jin ƙarin bayani….