News
Ƙone dazukan arewa ne kawai zai yi maganin aiyukan ƴan fashin daji — El-Rufai
Daga Yasir sani Abdullah
Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya bayar da shawarar a ƙona dazukan arewa domin kakkabe ɓarayin daji da suka addabi yankin.
“Na sha faɗa cewa, abin da ya kamata shi ne a ƙona dajin, a kashe su gaba ɗaya, daga baya mu sake shuka bishiyoyi,” kamar yadda gwamna El-Rufai ya shaidawa kafar Arise TV a wata hira ta musamman.
Ya ƙara da cewa ƙona dajin ne kawai mafita duk da matakin zai shafi waɗanda ba su ji ba su gani ba.
“Ya fi a kakkabe su a dawo da zaman lafiya mutane su koma noma,” in ji shi.
Ya ce yadda ake tunkararsu ba zai kawo ƙarshen matsalar ba – “domin idan an kore su daga Sokoto, za su tsere su tsallaka Kebbi.”
“Abin da za a yi kawai a yi masu ruwan wuta ta sama da ƙasa a dukkanin jihohi shida na arewa maso yammaci da Neja.”
“Idan aka yi haka ina ganin cikin makwanni ana iya maganin matsalar ”