News
HOTUNA: Jonathan ya kaiwa Buhari ziyara yayin da a ke raɗe-raɗin zai koma APC
Daga kabiru basiru fulatan
Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan ya kaiwa Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ziyara a fadar sa 5a villa yayin da a ke raɗe-raɗin cewa zai sauya sheka zuwa Jam’iya mai Mulki ta APC ya kuma tsaya takarar shugaban ƙasa a 2023.
Duk da cewa Jonathan ya ga Buhari ne domin bashi bayanai a kan yanayin siyasa a Mali, wasu na ganin cewa zuwan na shi na da nasaba da harkar sa ta siyasa.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa wasu ƙusoshi a APC na ƙoƙarin jan hankalin Jonathan ya koma APC domin ya tsaya takarar shugaban ƙasa ya kammala zangon mulkin sa na biyu.
A tuna cewa, a zaɓen 2015 Jonathan ya sha ƙasa a hannun Buhari, in da tsohon shugaban kasar bai yi musu ba ya sauka ya danƙawa shugaban na yanzu mulki.
Tun bayan zaɓen sai Jonathan ya rage shiga harkokin siyasa in da ko babban taron gangamin jam’iyar PDP ma bai je ba.