Connect with us

News

Buhari ya yabawa Ganduje a kan addu’o’in zaman lafiya

Published

on

Spread the love

Daga Yasir sani Abdullah

 

Shugaba Buhari wanda ya samu wakilcin wakilcin ministan ma’aikatar ayyukan gona, Alhaji Mustapha Baba Shahuri.

Advertisement

Ya ce, an shirya taron a dai-dai lokacin da ya da ce, inda ya ce dama addu’a ce kadai hanyar maganin matsalolin kasar nan.

ya bayyana hakan ne yayin taron yiwa Kasa addu’a wadanda Gwamnatin Jihar Kano ta Shirya da nufin Samun saukin Matsalolin tsaro da ake fuskanta a Wasu jihohin Kasar nan.

A jawabinsa gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce, an shirya taron ne domin kaskantar da kai ga Allah tare da rikonsa ya kawowa Najeriya saukin matsalolin da a ke fuskanta.

Advertisement

Ya kuma bada tabbacin duk shekara gwamnatin za ta rikka shirya taron kamar yadda shugaban kasa ya bukata, tare da yin roko ga Sheikh Dahiru Usman Bauchi da ya amince da bukatar gwamnatin Kano na gudanar da mauludin Shehu Ibrahim Inyas na kasa a Kano.

Gwamna Ganduje ya godewa duk mahalatta taron musamman Khalifan Tijjaniya na Duniya Sheikh Sidi Ali Bil Arabi da ‘yan tawagar sa bisa halartar Kano da su kai, domin yi wa Najeriya addu’o’in samun zaman lafiya.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana lokacin taron Addu,a da gwamnatin Kano ta shirya a filin wasa na Sani Abacha da ke nan kano.

Advertisement

Da ya ke nasa jawabin sa, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, bayan ya yabawa gwamna Ganduje,ya kuma bada tabbacin za su kawo Mauludin Sheikh Ibrahim Inyas na wannan shekarar Kano kamar yadda Gwamnan ya roka.

Sheikh Dahiru Bauchi ya kuma yabawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kan yadda ya ke kokari wajen inganta tsaro a kasar nan.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *