News
Ɗaliban Kano 80,000 ne su ka lashe dukka maki 9 a jarabawar NECO – Gwamnati
Daga Yasir sani Abdullah
Gwamnatin Jihar Kano ta ce ɗalibai 80,000 ne su ka samu nasarar cin dukkan maki 9 a jarabawar NECO da su ka rubuta a shekarar 2021.
Kwamishinan Ilimi na jihar, Sanusi Sa’idu-Kiru ne ya bayyana hakan, a wani taron manema labarai kan nasarorin da ma’aikatar ta samu a shekarar 2021.
Ya ce, “Jihar Kano ce ta fi kowacce yawan dalibai da su ka za na jarrabawar kammala sakandare ta (SSCE) a kasar nan. Mu na da dalibai 89,000, wadanda su ka zana jarabawar NECO a shekarar 2021; daga cikin wannan adadin, kusan 80,000 ne suka samu maki tara, wanda ya nuna cewa mun samu nasarar jarabawar kashi 95 cikin 100 a NECO”.
A cewar kwamishinan, “Gwamnati ta kashe Naira miliyan 235 wajen biyan kudaden jarrabawar wasu daga cikin ‘yan dalibai.
Ya kuma kara da cewar,”Kananan hukumomi 44 da ke jihar, ‘yan majalisar dokokin jihar da na majalisar dokoki ta kasa da kuma masu hannu da shuni, suma sun kashe kimanin Naira miliyan 500 wajen biyan kudaden jarabawar ga dalibai”.
Sa’idu Kiru ya bayyana cewa jihar, ta na da makarantun firamare sama da 7,000 da kuma makarantun sakandire 1,517 a fadin kananan hukumomin jihar 44.
Haka zalika,“ Gwamnati ta kara daraktocin shiyya na manyan makarantun sakandire daga 14 zuwa 23, na SUBEB daga 10 zuwa 15 da kuma hukumar kula da ilimin jama’a daga 10 zuwa 15.
“Ga cibiyoyi masu zaman kansu da na sa kai, bakwai da a ka kafa, hukumar dakin karatu, makarantun kimiyya da fasaha sun samu uku. Domin haka, yanzu muna da ofisoshin shiyya 66 a duk fadin jihar da ke karkashin ma’aikatar MDAs.
“An amince da Naira dubu dari ga kowane shiyya a matsayin kudin gudanar da ayyukan sa ido da kula da makarantun,” in ji shi.
Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnati ta iya daukar ma’aikata 5,700 da suka cancanci ilimi daga ma’aikatu da ma’aikatu da hukumomi zuwa aikin koyarwa a aji.
Ya kara da cewa karin malamai 6,995, wadanda ke karbar albashin gwamnati, amma su na koyarwa a makarantu masu zaman kansu da na al’umma an kuma dawo da su koyarwa a makarantun gwamnati a jihar.
Sa’idu Kiru ya ce gwamnati ta kashe miliyoyin Naira wajen siyan litattafai miliyan daya.Gwamnati za ta ci gaba da samar da tsare-tsare da kayayyakin koyarwa a makarantun, domin inganta koyo da koyarwa, hakan zai sa iyaye da dama su tura ‘ya’yansu makarantun gwamnati.